
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Wata kotu a Faransa ta yanke wa wani malamin Shi’a haifaffen Iran hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari bayan ta same shi da laifin taimaka wa ‘yan ci-rani ketarawa zuwa Ingila ta hanyar kananan kwale-kwale.
Kotun ta kuma yanke wa wani mutumin dan darikar malamin wanda suke harkar tare zaman gidan sarkar na wa’adin da bai kai na malamin ba.
Tun a watan Disamba ‘yan sanda suke sa ido kan ayyukan Mohamed Baraeikechi-Ghaleshi, mai shekara 39, wanda malamin ‘yan Shi’a ne a birnin Rouen na Faransar.
Sai a watan Afrilu ne jami’n tsaron suka damke shi tare da daya mutumin, a kan cewa suna taimaka wa masu fafutukar shiga Ingila daga Faransa.
An zargi mutanen biyu da samar da kwale-kwale irin wanda ake hura wa iska, guda 6 ko 7, masu daukar kusan mutum takwas-takwas kowanne, wadanda suke tashi daga kusa da yankin Calais na kasar.
Ba a dai san kwale-kwalen har guda nawa ne suka samu nasarar wucewa suka shiga kasar ta Ingila ba.
Masu gabatar da karar sun sheda wa kotun cewa malamin yana hulda da kungiyoyin masu safarar jama’a, kuma ana ba shi kamasho a duk kwale-kwale daya da ya yi hanya aka saya.
Tun shekarar da ta wuce yawan mutanen da ke kokarin ketarawa daga yankin zuwa Ingila a kananan jiragen ruwa ko kwale-kwale ya karu sosai, kuma yawancin mutanen ‘yan Iran ne.