An Tsinci Gawar Yaron da a ƙwaƙule Masa ido a Jigawa

An tsinci gasar wani yaro Almajiri mai shekaru 16 Yusufa Mustapha, bayan wasu ‘yan bindiga sun zare idonsa daya a karamar hukumar Kiyawa ta jihar, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana.

An ruwaito cewa malamin da lamarin ya shafa, Malam Mustafa, da ke unguwar Abuja, ya kai rahoto ga hukuma, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa.

Ya kara da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Mustapha ya yi tattaki zuwa wani daji da ke makwabtaka da shi domin samo itace da karfe 8 na safe.

Malamin ya yi ikirarin cewa marigayin wanda bai koma gida ba kamar yadda aka tsara, daga baya an gano shi kwance a cikin wani tafki na jini ba tare da idonsa daya ba.

More from this stream

Recomended