An tsinci gawar yarinya ‘yar shekara 16 da aka jefa rijiya a Jigawa

An jefar da gawar wata yarinya ‘yar shekara 16 a cikin rijiya da ke karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.

Wani dan uwan mamaciyar da ya sakaye sunansa, ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Beguwa a ranar Asabar din da ta gabata.

Ya ce an fara bayyana cewa marigayiyar ta bace kafin a gano gawarta a ranar Laraba, kwanaki hudu bayan faruwar lamarin, yayin da wasu manoma da ke kan hanyarsu ta zuwa gona suka ji wani wari.

Ya ce tare da taimakon hukumar kashe gobara, jami’an tsaro, da samari nagari, an dauki gawar tare da binne ta bisa ga shari’ar Musulunci.

Ya yi zargin cewa saurayinta da abokansa ne suka yi wa marigayiyar fyade, inda suka jefar da gawarta a cikin wata rijiya da ke wajen kauyen.

More from this stream

Recomended