An tsaurara matakan tsaro gabanin ziyarar Buhari a Lagos

An tsaurara matakan tsaro a birnin Lagos gabanin zuwan shugaban kasa Muhammad Buhari.

An jibge tarin jami’an tsaro daban-daban a wurin sauka da tashin shugaban kasa dake filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Lagos.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa shugaban kasa Buhari zai kai ziyara daga ranar 23 ga watan Janairu zuwa 24 inda zai kaddamar da wasu ayyuka daban-daban.

Sojojin sama, sojojin ruwa, jami’an tsaron Civil Defence da yan sanda na daga cikin jami’an tsaron da aka girke a wurare na musamman daban-daban a jihar.

A cikin ayyukan da Buhari zai kaddamar sun haɗa da tashar jiragen ruwa, layin jirgin kasa, kamfanin shinkafa da kuma cibiyar Randle ta yada tarihi da al’adun Yarabawa.

More from this stream

Recomended