An tsaurara matakan tsaro a majami’un Ghana

'Yan sandan Ghana

Hakkin mallakar hoto
BBC.com

An tsaurara matakan tsaro a coci-coci a kasar Ghana don kariya a kan abinda shugabannin kirista a kasar suka ce ana kara samun barazanar hare-haren ta`addanci daga masu kaifin kishin islama a yankin Afirka ta yamma.

A kwanakin baya ne dai wasu masu ikirarin jihadi suka kai harin ta`addanci a wasu majami’u da ke kasar Burkina Faso mai makwabtaka da kasar ta Ghana.

Barazanar da ta sa shugabannin addinin kirista a Ghana suka gudanar da wani taro da hukumomin tsaro don daukar matakan kare yi wuwar afkuwar hakan a kasar.

An dai tsaurara matakan tsaron ne domin kasancewa cikin shiri don fuskantar barazanar da ke tasowa.

Daga cikin matakan tsaron, akwai haramta shiga cikin coci da jakar nan da ake ratayawa a baya, sannan kuma za a rinka girke jami’an tsaro a wajen shiga majami’un kasar a duk ranar Lahadi.

A kwanakin baya ne dai wasu masu kaifin kishin islama suka kai wasu hare-hare a wasu majami’u da ke arewacin kasar Burkina Faso wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

Wadannan hare-haren da aka kai Burkina Fason ne ya tilasta wa wasu barin kasar inda suka kwarara zuwa kasar Ghana a matsayin ‘yan gudun hijira.

Ana dai ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci na masu ikirarin jihadi a yankin yammacin Afirka lamarin da ya sa ake ci gaba da yunkurin karfafa matakan taro a nahiyar.

More from this stream

Recomended