An tabbatar da mutuwar mutane 6 a hatsarin jirgin kasa a Lagos

Mutane 6 aka tabbatar da mutuwar su a hatsarin jirgin kasar da ya rutsa da wata babbar motar fasinja a jihar Lagos.

Hatsarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis wajen unguwar Shogunle da Ikeja lokacin da motar ta nemi tsallaka layin dogon inda ta ci karo da jirgin dake tawowa.

Fasinjoji da dama ne suka jikkata a hatsarin inda aka kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Lagos.

Da yake magana da yan jaridu a asibitin koyarwar, gwamnan jihar Babajide Sanwoolu ya ce an tabbatar da mutuwar huɗu daga cikin mutanen a asibitin.

Tun da farko an bada rahoton cewa biyu daga cikin mutanen da abin shafa sun mutu nan take a wurin da hatsarin ya faru.

Gwamnan ya kuma nemi jama’a da su bayar da tallafin jini a marasa lafiya.

More from this stream

Recomended