Ronald Koeman ba zai ja ragamar Barcelona ba a wasan La Liga ranar Asabar da za ta fafata da Atletico Madrid a Camp Nou.
Hakan ya biyo bayan rashin nasara da kungiyar ta yi , bayan daukaka karar dakatar da kocin wasa biyu da hukumar kwallon kafar Spaniya ta hukunta shi.
An kori Koeman a wasan da Granada ta doke Barcelona da ci 2-1 a Camp Nou ranar 29 ga watan Afirilu, bayan fadin kalamai na rashin da’a ga alkalin wasa mai jiran ko-ta-kwana.
Tun farko kwamitin gasar La Liga na hukumar kwallon kafar Spaniya ya dakatar da kocin wasa daya nan take daga baya ya kara hukuncin zuwa karawa biyu.
Kocin dan kasar Netherland bai ja ragamar kungiyar wasan da ta doke Valencia 3-2 a gasar La Liga ba ranar Lahadi.
Mataimakin Koeman, Alfred Schreuder shi ne zai ja ragamar Barcelona a fafatawar da za ta yi da Atletico Madrid ranar Asabar.
Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 74, iri daya da na Real Madrid wadda take ta biyu.
Atletico Madrid ce ta daya a kan teburi da maki 76, kuma saura wasa hurhudu a karkare kakar bana.