An Soma Taron Majalisar Manoman Najeriya, Karo Na 43

A jiya Talata aka fara taron majalisar manoma ta Najeriya karo na 43 a Umuahiya hedikwatar jihar Abia da ke kudu maso yammacin Najeriya, don inganta noma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Da yake jawabinsa a gurin taron, Dakta Aminu Babandi, wanda ya wakilci Dakta Mohammed Bello Umar, babban Sakataran Ma’aikatar Noma na Tarayya ya ce, dole ne a bunkasa noma tare da tabbatar da cewa man kirkiro shirye-shiryen da za su samu goyon baya a matakan jihohi da kuma tarayya.

Babandi ya kuma kara da cewa suna duba gurare guda uku inda za su fi mayar da hankali.

Shima Kwamishinan Noma na jihar Abia, Barista Chinedum Elemchi, ya bayyana farin cikinsa lokacin da yake jawabin bude taron, inda ya ce gwamnati tasha kaddamar da shirye-shirye a kokarinta na inganta harkar noma a duk fadin kasar.

Sannan ya kuma ce ya kamata a tattaro sakamakon wadannan shirye-shiryen don dubasu da kyau domin bunkasa tattalin arziki da kuma samar da aikin yi.

Haka kuma taron ya samu halartar mutane daga fannoni daban daban na rayuwa a kokarin da ake na tsara dabarun inganta noma don bunkasa tattalin arzikin kasar.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...