
Kasar Cyprus ita ce koma baya a haifar yara, inda mace kan haifi Da daya tilo
Rahoton da masu binciken suka fitar, ya nuna kusan rabin karni guda kenan da ake haifar yara nan da can hakan kuma ya janyo koma baya da rasa hanyar da za a cike gibin.
Rahoton da aka wallafa a mujallar lafiya ta Lancet, ya yi nazari daga shekarar 1950-2017, inda aka gano akalla mata na haifar yara kusan 4-7 amma yanzu lamarin ba haka ya ke ba.
Masu binciken sun ce kasar Cyprus ita ce ta fi kowacce karancin yara a duniya inda mata kan haifi Da daya tilo.
Ya yin da jamhuriyar Niger aka samu raguwar haihuwar amma ba kamar yadda ake gani a kasashen turai ba. Rahoton ya ce abin damuwar shi ne za a samu al’umar da babu yara kanana a ciki sai tsofaffi.
Kasashen da suke cikin hadarin rashin yara sun hada da Turai, da Amirka, da Koriya ta Kudu, sai kuma kasar Australia.
Farfesa Murayya na daga cikin masu binciken, ta kuma matsalar ba ta da alaka da rashin karfin maniyyin maza ko na kwayayen haihuwa.
amma ta ce abubuwa uku ka iya janyo matsalar, wadanda suka hada da raguwar mutuwar mata ya yin haihuwa, da samun maganin tsarin iyali a saukake da kuma yadda mata ke neman ilimi da jajircewa wajen yin aiki ko na gwamnati ko mai zaman kansa.
A karshen rahoton ya ce an samu raguwar ne saboda yadda mata suke fitowa ake damawa da su ta fuskar ayyuka, da ilimi da uwa uba samun maganin tsarin iyali a saukake ba ga matan birane kadai ba har da yankin karkara.