A Najeriya cibiyar kare cututtuka masu yaduwa, wadda ake kira NCDC a takaice, ta bayyana cewa a watanni ukun farko na wannan shekarar, an samu karuwar mutanen da suka kamu da zazzabin Lassa wanda bera ke haddasawa.
A shekarar bara a daidai wannan lokaci ne aka samu bayanin kamuwa da cutar zazzabin Lassa har sau 1801.
Daga ciki, mutum 114 ne suka mutu sanadiyyar zazzabin a jihohi 21, a yayin da a wannan shekarar, a watanni ukun farko, alkaluma na nuni da cewar an samu rahoton kamuwa da zazzabin Lassa har sau 3735.
Wassu mata da ke jinyar ‘yar uwarsu sun shaida wa wakilin Muryar Amurka cewa ana nuna musu kyama da tsangwama.
“Ba a dauki masu cutar da wani muhimmanci ba, maimakon a taimaka musu yadda ya kamata amma sai ka ga gudunsu ma ake yi,” a cewarta.
Daga cikin mutane 3735 da aka samu labarin cewa suna dauke da cutar, an tabbatar da guda 906, a yayin da mutane 161 su ka mutu a sanadiyar zazzabin a jihohi 27.