An samu gobara a matatar mai ta  Dangote

Gobara ta ƙone wani sashe na matatar man fetur ta Dangote.

Lamarin ya faru ne a ranar  Larabar.

Da yake magana da manema labarai, Anthony Chijiena mai magana da yawun rukunin kamfanonin Dangote ya ce gobarar ta kama ne a sashen da ake tace gurbataccen ruwa dake matatar.

Ya ce tuni aka shawo kan wutar ya ƙara da cewa gobarar bata yi muni sosai ba.

Ya ƙara da cewa babu damuwa sosai domin matatar na cigaba da aiki kamar yadda aka saba.

A ranar 12 ga watan Yuni ne matatar ta Dangote ta fara aiki ka’in dana in inda aka fara ta ce man Diesel da kuma na jirgin sama.

More News

Ƴansanda a Kaduna sun kama ƴan fashi da masu garkuwa da mutane sama da 170

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun kama wasu mutane 143 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ‘yan fashi da makami...

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Biyu Daga Hannun Ƴan Fashin Daji A Sokoto

Dakarun rundunar sojan Najeriya dake aikin yaƙi da ƴan ta'adda a jihar Sokoto sun samu nasarar daƙile yunkurin yin garkuwa da mutane inda suka...

Fasto na neman a taimaka masa ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga

Micah Sulaiman limamin majami'ar St. Raymond Catholic Church dake Damsa a Gusau jihar Zamfara ya roƙi a taimake shi domin ya samu ƴanci. A wani...

An yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Hajiya Halima Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa, Dauda Adamu da aka fi sani da Rarara.Rahotanni sun nuna...