An samu fashewar nakiyoyi a wurin taron yakin neman zaben APC

Wasu abubuwan fashewa da ake kyautata zaton nakiyoyi ne sun fashe a wurin gangamin taron jam’iyyar APC a jihar Rivers.

Magoya bayan jam’iyar ta APC da dame ne suka jikkata sakamakon fashewar da ta faru a filin Igboukwu dake Fatakwal.

Da yawa daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su mata ne kuma anyi gaggawa garzayawa da su asibiti.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan musabbin fashewar amma wasu rahotanni sun bayyana cewa tun da farko sai da aka samu sabani tsakanin al’ummar Rumoji dake da iko da filin wasan da kuma yan jam’iyyar APC kan izinin gudanar da taro a wurin.

Rahotanni sun bayyana cewa tun da farko matasa sun hana yan jam’iyyar ta APC isa wurin taron.

More from this stream

Recomended