Dogayen layukan mai sun sake bayyana a biranen Abuja da kuma Legas.
An ga motoci a layukan mai a ranar Litinin inda suke jira su sha mai a wasu gidajen mai a yayin da wasu gidajen man suke a rufe..
Akwai dogon layin a gidan mai na kamfanin NNPCL dake kusa da hedkwatar cocin Dunamis.
Haka ma abun yake a gidan mai na Total Energies dake unguwar Lugbe.
Gidajen man Shema da NNPCL dake kan titin Karu dukkansu na rufe.
A birnin Lagos ma an ga dogayen layuka a wasu gidajen mai da suke da man a birnin.
Da yake magana kan halin da ake ciki, Clement Isong sakataren kungiyar MEMAN ta manyan dillalan makamashi ta Najeriya ya faɗawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa jinkiri da aka samu wajen ɗauko man daga depo shi ne musabbabin ƙarancin man.