An sako wani alƙali a jihar Borno bayan shafe wata biyu a hannun ƴan bindiga

An sako mai Shari’a Haruna Mshelia alƙalin babban kotun jihar Borno wanda aka ɗauke a cikin watan Yuni.

Daso Nahum mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Borno ya bayyana cewa, Mshelia na tafiya tare da matarsa, direbansa, da kuma dogarinsa lokacin da lamarin ya faru akan hanyar Maiduguri zuwa Biu.

Wani saƙo da aka wallafa a manhajar WhatsApp   a dandalin  ƙungiyar lauyoyi ta NBA reshen jihar Borno ya tabbatar da sako alƙalin.

“Alhamulillah yanzu muke samun labarin sakin mai sharia Haruna Mshelia,” a cewar saƙon.

Amma kuma har yanzu matarsa da direbansa na can riƙe a hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.

Saƙon da aka wallafa ya buƙaci a cigaba da addu’a domin suma su dawo gida lafiya.

More from this stream

Recomended