An Sako Mutane 7 Daga Fasinjojin Jirgin Kasar Da ‘Yan Bindiga Suka Kama

‘Yan bindigar sun sako mutanen bakwai ne sa’o’i kadan da cikar wa’adin kwanaki biyu da su ka bayar na fara yanka mutanen da su ka sace.

Daga cikin mutanen bakwai da ‘yan bindigar su ka saki akwai Dr. Muhammad Abuzar wani dan kasar Pakistan, da wata mace daya Bosede Olurotimi. Sauran wadanda aka sakin sun hada da Sadiq Abdullahi dan tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello kuma shugaban kungiyar dattawan arewacin Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi, da Aliyu Usman, da Abubakar Zubairu, da Alhassan Sule, da kuma Daiyabu Paki Tsohon shugaban karamar hukumar Ikara kuma shugaban wata hukuma a jahar Kaduna.

Wasu daga cikin mutanen da 'Yan Bindiga suka saki tare da Mallam Tukur da danginsu
Wasu daga cikin mutanen da ‘Yan Bindiga suka saki tare da Mallam Tukur da danginsu

A hirar ta da Sashen Hausa, daya daga cikin dangin Sadiq da ta nemi a saya sunanta ta bayyana cewa, basu biya kudin fansa ba kafin aka sake su. Ta kuma bayyana cewa, duk da yake, ya rame kwarai, yana magana cikin raha, abinda mai yiwuwa alama ce cewa, ba a gasa masu akuba ba.

‘Yan bindigar dai sun sha yin barazanar cewa za su kashe mutanen idan gwamnati ba ta biya bukatar da suka gabatar na neman musanyar wadanda suke garkuwa da su da ‘yan bindigar da gwamnati ta ke tsare da su ba.

Ko a ranar 24 ga watan Mayu sai da ‘yan bindigar su ka yi barazanar kashe mutanen a cikin kwanaki 7 idan gwamnati ba ta biya bukatun nasu ba na sakin “yaran su” da ke hannun rundunar sojin Najeriya ba.

Sadiq Ango Abdullahi, danginsa, da Mallam Tukur Mamu
Sadiq Ango Abdullahi, danginsa, da Mallam Tukur Mamu

Bayanai na nuni da cewa, kokarin wani mawallafin jarida Mallam Tukur Mamu ne ya kai ga sakin mutanen. Bisa ga cewar sa, duk da ya ke ya yi barazanar janyewa daga shiga tsakanin domin gaza samun goyon bayan daga gwamnati, ya sake komawa sabili da tausayin dangin wadanda su ke hannun ‘yan ta’addan.

A hirar shi da manema labarai jim kadan bayan sako fasinjojin, Malam Tukur Mamu ya ce shi kadai ya yi kokarin ceto wadannan mutane bakwai tare da taimakon mai gidan shi Sheikh Ahmad Gumi kuma ya ce ya dankawa sojoji wadannan mutane.

Kafin sada mutanen da danginsu, sai da aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu

Wani dattijo da 'Yan Bindiga suka saki da iyalansa
Wani dattijo da ‘Yan Bindiga suka saki da iyalansa

Ko a ranar 11 watan Yuni, sai da Mallm Tukur ya shiga tsakani aka samu sakin wadansu mutane 11 daga cikin mutanen da ‘yan bindigar ke garkuwa da su.

Idan za a iya tunawa, ‘yan bindigar sun kai hari ne kan jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna-Abuja ranar 28 ga watan Maris na wannan shekarar su ka tasa keyar fasinjoji sama da 60, adadin da hukuma ba ta tabbatar ba. Daga bisani, ‘yan bindigar su ka saki a wani dan kasuwa da aka saki bisa dalilan rashin lafiya, bayan sakin wata mace mai tsohon ciki da ta ce ‘yan bindigar sun sake ta bisa dalilan jinkai.

A halin yanzu dsi ‘yan bindigar na rike da kimanin fasinjoji 43.

Dan kasar Pakistan da 'yan bindiga su ka saki
Dan kasar Pakistan da ‘yan bindiga su ka saki

Akalla mutane takwas ne aka kashe a wannan harin da ‘yan bindigar su ka kai hada da , Amin Mahmoud, shugaban matasa na jam’iyyar APC, da wata likiciya Chinelo Megafu Chinelo wadda a lokacin kai harin ta wallafa a shafinta na twita cewa, an kaiwa jirgin hari kuma an harbe ta. Tana neman addu’a, kafin mutuwarta.

More News

Peter Obi Ya Ziyarci Mutanen Da Su Ka Ƙone Sakamakon Wutar Da Wani Ya Cinnawa   Masallaci A Kano

Ɗan takarar shugaban ƙasa  a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam'iyar Labour Party (LP) Peter Obi ya ziyarci mutanen da wani matashi ya cinnawa wuta a...

An sanar da zaman makoki na kwana biyar saboda mutuwar shugaban kasa a Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da zaman makoki na kwanaki biyar saboda rasuwar shugaban kasar Ibrahim Raisi...

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...