An sako malamai da ‘ya’yansu da aka sace daga Jami’ar Abuja

Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa ‘yan bindigar da suka sace wasu malamai da ‘ya’yansu daga Jami’ar Abuja sun sake su.

Wata sanarwa da Jami’ar Abuja ta fitar ranar Juma’a ta tabbatar da sako ma’aikatan nata da aka yi garkuwa da su ranar Talata.

Sanarwar, wacce shugaban jami’ar ya fitar, ta ce haɗin gwuiwar jami’an tsaron Najeriya da ta hada da sojoji da ƴan sanda da jami’an DSS ne suka ceto duka mutanen.

More from this stream

Recomended