An sako karin mutane uku daga cikin fasinjojin jirgin kasar Abuja-Kaduna

Yan bindiga sun sako karin mutane uku daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su a jirgin kasar da ya ta shi daga Abuja zuwa Kaduna .

A cikin wata ganawa da yayi da gidan rediyon BBC Hausa daya daga cikin mutanen da aka sako ya ce bashi da masaniyar biyan kudin fansa kafin a sako su.

Ya bayyana cewa sun sha bakar ukuba a hannun yan bindiga a kwanakin da suka shafe a hannunsu.

Sakin nasu na zuwa ne sama da wata hudu bayan da yan bindigar suka sace su akan hanyar su ta komawa daga Abuja zuwa Kaduna.

More from this stream

Recomended