Wasu mazauna garin Suleja dake jihar Niger sun fantsama kan tituna domin yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasarnan.
Da yake magan da jaridar The Cable ranar Laraba, Sadiq Suleja dan takarar majalisar jiha karkashin jam’iyar PRP a mazabar Suleja ya ce masu zanga-zangar sun taru inda suka fara ta da karfe 9 na safe.
Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye da aka rubuta cewa “Yan Najeriya Na Shan Wahala A Kawo Karshen Wahalar Yanzu”.
A cewar Sadiq zanga-zangar da aka gudanar takaitacciya ce kuma bata samu halartar mutane masu yawa ba.
Wannan karo na biyu da ake makamanciyar irin wannan zanga-zangar a jihar Niger biyo bayan wacce aka yi a ranar Litinin.