An saka dokar hana fita a Kano

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a jihar domin kaucewa tabarbarewar doka da oda biyo bayan korar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigerian People’s Party da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar ta yi.

An tsaurara matakan tsaro a duk fadin birnin Kano a ranar Laraba jim kadan bayan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ta ayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris 2023. a

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Gumel, wanda ya tabbatar da dokar hana fita a cikin wata sanarwa, ya ce dokar ta fara aiki ne daga karfe 6 na yammacin Laraba zuwa karfe 6 na yammacin ranar Alhamis (yau). Gumel ya sha alwashin tabbatar da bin umarnin da aka ba su, inda ya yi gargadin cewa za a kama wadanda suka saba wa doka kuma su fuskanci fushin doka.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...