An saka dokar hana fita a Gombe

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin jihar Gombe ta saka dokar hana fita a birnin jihar bayan an samu fargabar tashin hankali a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu arangama ne bayan an dauko gawarwakin ‘yan kungiyar nan masu fareti da kade-kade na Boys and Girls Brigade da aka kashe a lokacin bikin Easter.

An bayyana cewa bayan dauko gawarwakin ne wasu matasa suka fara jefe-jefe da kokarin tayar da zaune tsaye a jihar.

A lokacin bikin Easter ne dai wani lamari ya faru a jihar ta Gombe inda wani direban mota ya yi ciki da wasu masu fareti kan titi domin murnar Easter.

An bayyana cewa ran direban ne ya bacci sakamakon tare hanyar da suka yi inda ya yi amfani da motarsa ya bige mutane da dama inda mutum tara suka mutu.

A wannan dalili ne ya sa jama’ar wurin suka farwa direban da fasinja daya da ke cikin motar inda suka kashe su har lahira.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Gombe Mary Mullum ta tabbatarwa BBC da saka dokar hana fitar.

More from this stream

Recomended