Mazauna kauyukan karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun koka game da ci gaba da kai hare-haren ta’addanci.
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace mutane 19 yawancinsu mata daga kauyen Madogara.
A cikin wannan samamen da aka kai cikin dare, an kama mata 16 da maza uku, tare da yara, wasu ‘yan kasa da shekara daya.
Wani jami’in lafiya daga garin Batsari da ya bukaci a sakaya sunansa saboda matsalolin tsaro, ya bayyana cewa a hankali Madogara ta koma baya.
Ya ce a kowane dare, mazauna kauyen na taruwa a gidajen tsakiyar kauyen don neman tsira kafin su koma gidajensu da safe.