An rantsar da Lalong a matsayin sanata

An rantsar da tsohon Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi, Simon Lalong, a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu.

Idan ba a manta ba tsohon ministan ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Talata.

An tabbatar da murabus din Lalong ne a wata sanarwa da mai ba wa minista mai barin gado shawara kan harkokin yada labarai, Dr Makut Simon Macham, ya sanya wa hannu.

More from this stream

Recomended