
Gwamnatin tarayya ta sanar da kwaso yan Najeriya 161 da suka maƙale a ƙasar Libya a kokarin su na zuwa cirani kasashen Turai.
A wata sanarwa ranar Talata, jakadan Najeriya a Libiya Kabiru Musa ya ce an kwaso mutanen ne tare da taimakon Hukumar Kula da Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin(IMO).
Musa ya ce kwaso mutanen da suke son dawowa dan kashin kansu an tsara shi ne domin tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da ya maƙale a ƙasar ta Libiya.
“Waɗanda aka kwaso sun baro filin jirgin saman Mitiga dake Tripoli a cikin wani jirgi da aka yi shata a ranar Talata kuma ana sa ran za su sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos a wani lokaci yau.” ya ce
“Waɗanda aka kwaso sun ƙunshi maza 37, mata 100 yara 16 da kuma ƴan kananun yara 8.”
Jakadan ya cigaba da cewa ofishin jakadancin da kuma sauran hukumomi na cigaba da wayar da mutane irin illar dake tattare da tafiya cirani da suka haɗa da bauta da kuma tilasta aikatau.