An kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Libya | BBC Hausa

A shafe watan

Hakkin mallakar hoto
AFP

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi Alah-wadai da harin bam da aka kai cikin wata a birnin Benghazi da kakkausar murya.

Ya ce tilas bangarori masu fada da juna su mutunta abin da ya kira shirin zaman lafiya domin jin kan al’umma — shirin da shugaban kungiyar ‘yan s akai Janar Khalifa Haftar da bangaren gwamnati suka ce suna mutuntawa a yanzu.

To bari mun fara da kasar Libya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da shirin tsagaita wuta da bangarori biyu masu fada da juna suka cimma domin mutunta bukukuwan Sallah babba.

Wannan yarjejeniyar tsagaita wutar ta biyo byan wani harin bam da aka kai da wata mota ne a birnin Benghazi ranar Asabar, wanda yayi sandiyyar mutuwar ma’aikata uku na Majalisar Dinkin Duniyar, kuma wasu faraen hula da ba a san adadinsu ba suka sami raunuka.

Dakarun janar Haftar ne ke iko da Benghazi, kuma wata hudu kenan yana kokarin kwace babban birnin kasar Trabulus amma babu nasara. Kakakinsa ya ce za su dakatar da kai hare-hare a yankunan da ke wajen birnin.

Amma gwamnatin kasar wadda ke da goyon bayan MDD ta ce dole ne a tsagaita wuta a dukkan yankunan da kawo yanzu ake gwabza fada.

Kwamitin tsaro na MDD yayi wani zama na gaggawa kan batun rikicin Libyan, kuma mataimakiyar Sakatare Janar na MDD, Bintou Keita ta ce MDD ba za ta fice daga kasar ba har sai ta ga an kawo karshen rikicin.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...