
Rundunar yan sandan Najeriya ta kori jami’an ta uku bayan da ta same su da saɓawa dokokin aikin rundunar.
Jami’an da aka kora sune ke bada kariya ga shahararren mawakin nan Dauda Adamu Abdullahi Rarara
Yan sandan sun fito ne daga runduna ta musamman dake bawa muhimman mutane kariya.
A kwanakin baya ne wani fefen bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta da ya nuna yan sandan na harbi sama lokacin da suka raka shahararren mawakin garinsu na Kahutu dake jihar Katsina.
Yan sandan da aka kora sun haɗa da Insifecta Dahiru Shuaibu, Sajan Isa Danladi da kuma Sajan Abdullahi Badamasi.