
Yan bindiga a ranar Talata sun kai hari kan ayarin motocin, Chimezie Ukaegbu kwamishinan ciniki, kasuwanci da zuba jari na jihar Abia inda suka kashe yan sanda biyu.
Ukaegbu na kan hanyarsa ta kai ziyarar aiki a rukunin shagunan Ekoha Plaza lokacin da ya bindigar suka bude wuta kan ayarin motocinsa.
Lamarin ya faru ne a mahadar Sameck dake kusa da kasuwar Ariaria.
A lokacin harin an kashe dan sanda daya dake tare da ayarin motocin.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Maureen Chilaka ta ce wani dan sanda dake wurin ya na wani aiki na daban shima ya mutu a wurin.