Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe wata mata a gidanta da ke Unguwar Kadawa a Kano.
Waɗanda suka kashe matar matar mai suna Rukayya sun ji wa ƴaƴanta biyu rauni.
Abin ɗaure kai game da yadda aka kashe ta shi ne babu wanda ya san takamaimai lokacin da lamarin ya faru, sai dai ana kyautata zaton sun shiga gidan ne bayan magariba a ranar Asabar.
Duk da cewar mazauna unguwar sun ki yarda BBC ta naɗi muryoyinsu, amma sun bayyana cewa akwai magina a jikin gidan da shagunan sayar da kayayyaki haka kuma a iya saninsu ba su ga shigar wani baƙo gidan ba haka kuma ba su ga fitar waɗanda suka gudanar da wannan aika-aika ba.