Ƴan bindiga a ranar Talata sun kashe wani makiyayi tare da shanu 50 da kuma tumakai a garin Fanzo dake ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.
Alhaji Dan-Azumi wanda ya rasa shanu 21 a harin ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewa an jikkata ƙarin wani makiyayin lokacin da yake kiwo a yankin.
“Ba zato ba tsammani ƴan bindigar suka farma yankin inda suka fara harbi. Sun kashe ɗaya daga cikin makiyayan suka kuma jikkata wani. Ƴan bindigar sun kuma yi awon gaba da shanu sama da 50. Wasu daga ciki sun mutu a yayin da aka yanka wasu saboda raunin harsashi.Hari ne babu gaira babu dalili.”
Amma kuma kwamandan shiya ta huɗu na rundunar samar da tsaro a jihar ya kira su taro inda ya nemi kada su kai harin ɗaukar fansa tare da basu tabbacin za a gudanar da bincike.
Dan-Azumi ya ƙara da cewa ” Mu ƴan ƙasa ne masu bin doka muna kira ga jami’an tsaro dake yankin da su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin gaban shari’a.Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su ƙwato shanun da aka sace.”
Shugaban ƙungiyar, Gan Allah Fulani Development Association (GAFDAN), Garba Abdullahi wanda shima ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi kira ga jami’an tsaro da su nemo tare da kamo masu laifin a kuma hukunta su domin hakan ya zama izina ga ƴan baya.