An kashe mutum 59 a Borno

Kungiyar Boko Haram

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani hari da mayaka masu da’awar kishin addinin Islama suka kai jihar Borno ya halaka mutum kimanin 59.

Wadanda lamarin ya faru kan idanunsu sun ce mayakan ‘yan kungiyar ISWAP – wani tsagi na Boko Haram sun kutsa kauyen Gubio inda suka budewa jama’a wuta tare da bi ta kan wasu al’ummar garin.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu da kuma rakuma.

Yankin na Gubio ya sha fuskantar irin wadannan hare-hare lamarin da ya sa al’ummar yankin suka yi shirin ko ta kwana domin kare kansu.

An shafe fiye da shekaru 10 hukumomi a Najeriya suna yaki da kungiyar Boko Haram – wacce ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da lalata dukiya ta miliyoyin naira.

Rikicin na Boko Haram wanda aka soma a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya fantsama zuwa bakwabtan kasashe kamar su Nijar, Chadi da kuma Kamaru.

Gwamnatin Buhari dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma kuma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.

More from this stream

Recomended

Mutane 7 Sun Rasa Rqyukansu, 53 Sun Jikkata Sakamakon Guguwar Iska a Jigawa

Akalla mutane bakwai sun rasa rayukansu, yayin da 53 suka jikkata bayan wata guguwar iska ta yi barna a kananan hukumomi 13 na jihar Jigawa. Rahotanni sun nuna cewa guguwar ta shafi gidaje 5,403 a cikin garuruwa 120, inda ta lalata makarantu sama da 47, asibitoci uku, ofisoshin ‘yan sanda biyu, gidajen zama da sauran […]