An kashe mutane uku a wani rikicin kabilanci a jihar Adamawa

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutane ukua wani rikicin kabilanci a kananan hukumomin Nuuman da Demsa dake jihar.

Rikici ya ɓarke ne a garuruwan Selti da Kpasham har ta kai ga an rasa rayukan mutane uku.

Amma a ranar Laraba jami’an ƴan sanda sun ce tuni al’amurra suka cigaba da gudana yadda suke a garuruwan da rikicin ya faru.

Kwamishinan ƴan sandan jihar,Dankombo Morris shi ne ya jagoranci tawagar jami’an da suka kai ziyarar duba abun da ya faru kana suka riƙa gudanar da sintiri har ta kai ga an dawo da doka da oda.

Kwamishinan ya shawarci mazauna yankin da suka kaucewa tayar  da rikici kana su cigaba da gudanar da mu’amalar su ta yau da kullum cikin zaman lafiya ba tare da tsoro.

More from this stream

Recomended