An kashe mutane 50 a Katsina

Mutum 50 ake fargabar an kashe sannan aka sace wasu da ba a san adadinsu ba sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Mazauna garin Yargoje sun faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa maharan sun afka wa ƙauyen ne tun ranar Lahadi da dare.

Gomman ‘yanfashi ne suka kutsa Æ™auyen da ke Æ™aramar hukumar Kankara, inda suka fara harbi a kan mai tsautsayi.

“Sun yi ta harbi a kan kowa da kowa, inda suka kashe mana mutum 50 ciki har da Æ™anina,” kamar yadda Hassan Ya’u ya bayyana ta waya.

Wani mazaunin Kankara mai suna Abdullahi Yunusa ya ce da kyar ya tsallake rijiya da baya, kuma hare-haren sun ci gaba har zuwa tsakar dare.

“Sun mayar da Æ™auyenmu wani filin kisa, kusan babu gidan da harin bai shafa ba,” in ji shi.

Mahukuntar jihar ba su ce komai ba zuwa lokacin haÉ—a wannan rahoton.

More News

Muna aiki tukuru don kawar da aikata manyan laifuka a Najeriya—Tinubu ga Daraktan FBI

A ranar Juma’a ne shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncin daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI), Christopher Asher Wray, inda ya...

Sojojin sun kama wani mai safarar bindigogi a jihar Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin  samar da  tsaro a jihar Filato sun ka ma wani mai safarar  bindiga da ake nema ruwa...

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya akan hanyar Abuja-Kaduna

Fasinjoji da dama ne aka bada rahoton an yi garkuwa da su bayan da ƴan fashin daji suka buɗe kan wata mota ƙirar bus...

Kotu ta yanke wa É—ansanda hukuncin kisa saboda laifin kisan kai

Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yanke wa Sufeta Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin...