Gamayyar kungiyoyin farar hula a Najeriya karkashin inuwar kungiyar Civil Society Joint Action Group ta ce an kashe akalla mutane 2,423, yayin da aka sace 1,872 cikin watanni takwas na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin a Abuja a madadin kungiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya kafa dokar ta-baci kan garkuwa da mutane da sauran nau’o’in ta’addanci.
Ya ce lokaci ya yi da shugaban kasa zai bai wa jami’an tsaro da domin magance matsalar rashin tsaro.
An yi nuni da cewa wadannan nau’o’in rashin tsaro sun kawo cikas ga tsaro da walwalar ‘yan Nijeriya kuma suna ci gaba da tabarbarewa tsawon shekaru.