Gwamnatin jihar Kaduna ta ce a kalla mutane 214 ne suka mutu sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, rikicin kabilanci da kuma daukar fansa a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Maris 2023.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ne ya bayyana hakan a cikin wani rahoto na 2023 da ya gabatar wa kwamitin tsaro na jihar.
Aruwan ya bayyana cewa an kashe maza 196, mata 14 da kuma yara kanana hudu, yayin da aka yi garkuwa da wasu 746 a tsawon lokacin da ake bitar.
Ya kuma ce har yanzu Kaduna ta tsakiya ne ke kan gaba a jerin yankunan da aka fi samun mace-mace, da kusan 115.
Da yake karbar rahoton, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro a jihohin Arewa maso Yamma da Neja.