
Makiyaya biyu mace da namiji aka bada rahoton an kashe su a wajejen garin Tahore dake ka karamar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.
Wasu makiyaya dake yankin sun ce an kashe makiyayan ne a wani kwanton bauna da aka yi musu aka harbe su lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Maikatako akan baburdinsu.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo wanda ya tabbatarwa da yan jaridu faruwar lamarin a Jos ya ce lamarin ya faru ne da maraice.
Shugaban na MACBAN ya bayyana sunayen Umar Saidu da Rashida Yakubu a matsayin wadanda aka kashe.
Da yake allawadai da kisan ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukan matakai domin kaucewa hare-hare na ramuwar gayya a yankin na Bokkos.
Babayo ya yi kira ga Fulani makiyaya da kada su dauki doka a hannunsu.