An kashe gawurtaccen ɗan bindiga Janari a wani harin sojan saman Najeriya a Kaduna

An kashe riƙaƙƙen dan fashin daji kuma mai garkuwa da mutane a tare da wasu muƙarrabansa a wani hari da sojan saman Najeriya suka kai ranar Asabar.

Mai magana da yawun rundunar sojan saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet shi ne ya bayyana haka a Abuja ranar Lahadi inda ya ce Janari da abokan ta’asarsa su ne ke da alhakin kai hare-hare da yin garkuwa da mutane a jihar Kaduna da kuma kan titin Kaduna zuwa Abuja.

Ya ce harin sama da bangaren sojan sama na rundunar ” Operation Whirl Punch” ya kai an amince tare da aiwatar da shi bayan da aka gano Janari da muƙarrabansa a wani wuri dake kusa da Gadar Katako a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Gabkwet ya ce shawagin tattara bayanai da jirgin ya yi ya gano cewa gungun ƴan bindigar suna tattaruwa domin kai hari ko kuma garkuwa da mutane abin yasa aka kai harin kenan.

Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa an kai hari makamancin haka a wata maɓoyar yan fashin daji dake Chukwuba a jihar Niger.

More from this stream

Recomended