An karrama DPO da yaki karɓar cin hancin $200,000

0

Babban sifetan yan sanda na kasa, Usman Baba Alkali ya karrama,SP Daniel Itse Ama babbban baturen yan sanda na ƙaramar hukumar Nasarawa dake jihar Kano.

Amah wanda aka rawaito yaki karbar cin hancin kuɗi dalar Amurka 200,000 kan wani laifi da ya shafi fashi da makami.

Laifin na aikata fashi da makami ya shafi wani lauya mai zaman kansa a Kano, da kuma wasu yan sanda guda biyu.

A cikin wata wasikar jinjina, da babban sifetan ya aika masa, ya yabawa Amah kan yadda ya nuna matukar kwarewa da ta kai ga kama, Ali Zaki lauya mai zaman kansa a Kano da kuma wasu yan sanda biyu.