HomeHausaAn Kara Farashin Man Fetur a Najeriya

An Kara Farashin Man Fetur a Najeriya

Published on

spot_img

Sanarwar karin kudin dakon Man fetur din wadda aka rabawa manema labarai na dauke da sa hannun Manaja mai kula da depot mai suna D.O Abalaka. Kuma kamfanin PPMC dake zaman wani reshe na ma’aikatar Man fetur ta kasa NNPC, wacce ita ma ta amince da karin.

Shugaban Kungiyar Man fetur masu zaman kansu ta IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingaru, ya ce samun takardar sanarwar ke da wuya, suka yi wa ‘yan kungiyar su umurni da cewa daga yanzu su sayar da Man fetur akan Naira 158 zuwa Naira 160 a kan kowacce lita daya.

Mai nazarin al’amuran yau da kullum Abubakar Aliyu Umar, ya ce gwamnati ta fito kiri kiri ta nuna rashin tausayi ga talakawa wadanda sune suka zabe ta. Ya kara da cewa a cikin yan watanni an yi kari har sau uku, ga annobar coronavirus ga hauhawar kudaden kayan masarufi, to da wanne talaka zai ji?

Amma ga tsohon mukaddashin shugaban Ma’akatan Man fetur ta Kasa Kwamarad Isa Tijjani, ya ce ba a karin kudin mai mafita ta ke ba, abin da ya kamata gwamnati ta yi shine tayar da matatun Man kasar idan ana so a samu sauki.

Wasu masu sayar da Man fetur a kasuwar bayan fagge sun baiyana cewa kafin a kai ga yin wannan karin, suna sayar da Man fetur lita goma a kan kudi Naira 1,800.

Sanarwar ta ce daga ranar biyu ga wannan wata na Satumba karin ya fara aiki, kuma an kaiyade kudin ne a bisa karfin farashin Mai a kasuwar duniya.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this