An kammala wasu gidajen ƴan gudun hijira a Zamfara

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure ta kasa ta kaddamar da wasu gidaje sama da 40 da aka kammala saboda ‘yan gudun hijira a Zamfara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar NCFRMI Tunde Oyasanya ya fitar ranar Litinin.

A jawabinsa yayin kaddamarwar, Mista Oyasanya ya ce Tijani Ahmed, kwamishinan tarayya na NCFRMI, ya ce aikin zai dawo da martaba jihar, da kuma farfado da mutane ga wadanda abin ya shafa.

Mista Ahmed ya ce magabatansa ne suka fara aikin na ‘yan gudun hijira da marasa galihu a fadin kasar inda shi kuma zai ƙara himma wajen aiwatarwa.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...