
Hukumar NDLEA dake yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi ta samu nasarar kama wata mata ɗauke da kwayar Tramadol a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Matar mai suna Lydia Lami Jatau an kama ta ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos akan hanyarta ta zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Bincike da jami’an hukumar suka gudanar ya nuna cewar matar ta fito ne daga karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna kuma ta na zaune ne a birnin na Istanbul.
Femi Babafemi mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ya ce matar ta bayyana cewa tayi haka ne domin ta biya kuɗin fansa har miliyan ₦5 na babarta da yan bindiga suka sace.