An kama wasu mutane dake tayar da rikici a ƙaramar hukumar Mangu

Jami’an rundunar Operation Safe Haven dake samar da tsaro a jihar Filato sun samu nasarar kama wasu mutane da suke zargi da haddasa rikici a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

A wata sanarwa jami’in hulda da kafafen yaɗa labarai na rundunar, Oya James ya ce an samu kai mummunan hari da kuma barnatar dukiya daga wasu matasa a Kerang dake karamar hukumar ta Mangu.

Ya ƙara da cewa matasan ba iya barnar kadai suka tsaya ba har sai da ta kai sun kai hari kan jami’an sojojin dake aikin tabbatar da bin dokar hana fita da aka saka yankin.

Sanarwar ta kara da cewa an samu makamai da dama daga hannun matasan da aka kama.

More from this stream

Recomended