An kama wani mutumi dauke da takardun naira na bogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 47 da haihuwa bisa zarginsa da mallakar takardun karya na naira.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da kama shi a ranar Juma’a, ya ce wanda ake zargin, mai suna Shola, an kama shi ne a ranar 17 ga watan Janairu, 2024, da misalin karfe 6:30 na yamma, a Apapa Under Bridge, Legas, bayan ya sayi kayayyaki na N7,000 a kasuwar Oba Abdulfatai Aromire Ojora, Ijora, da takardun naira na bogi.

Hundeyin ya ce an mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda daga sashen ‘yan sanda na Ijora Badia inda aka samu karin naira 6,000 na bogi daga hannun sa.

“Jimillar kudaden da ake zargin jabun naira ne da aka kwato kamar yadda aka nuna sun kai N13,000. Daga nan ne aka mika karar zuwa sashen bincike na CID na jihar aYaba, Legas, don ci gaba da bincike.”

More from this stream

Recomended