An kama wani Fasto da laifin kashe matarsa har Lahira

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ekiti ta kama wani fasto na cocin Christ Apostolic Church, Abiodun Sunday, bisa zargin kashe matarsa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da kisan matar Fasto, Tosin Oluwadere, a Ido-Ile a karamar Hukumar Ekiti ta Yamma ta Jihar Ekiti a ranar Alhamis.

Kakakin ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan kisan.

An tattaro cewa wanda ake zargin limamin coci ne kuma likitan gargajiya.

Wani dan’uwan mamaciyar, Mista Samuel Ibironke, ya yi zargin cewa, “Bayan ya kashe ƙanwata, sai ya kira matata wadda ma’aikaciyar lafiya ce ta zo ta taimake shi, sai matata ta isa wurin ta gano cewa ya shake kanwata har lahira.”

More from this stream

Recomended