An kama wani fasinja bayan da ya saci miliyan 1 a cikin jirgin

Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya ce an kama wani fasinja da aka samu da satar kudi naira miliyan 1 daga cikin jakar wani fasinja da shima yake cikin jirgin kamfanin.

Stanley Olisa mai magana da yawun kamfanin a wata sanarwa ranar Laraba ya ce lamarin ya faru ne jirgin saman kamfanin da ya tashi daga Abuja zuwa Fatakwal a ranar 27 ga watan Yuli.

Olisa ya ce an samu nasarar kama wanda ake zargin da taimakon ma’aikatan jirgin da kuma mutumin da ya yiwa satar.

Ya kara da cewa mutumin ya kuma dauki komfuta laptop ta wani fasinja duka dai a cikin jirgin.

More from this stream

Recomended