An kama wani mutum mai suna Chinedu Ezeudu dan asalin kauyen Ndi Ikpa Ezinato da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra da laifin sayar da hotuna da bidiyon wata mata tsirara a shafukan sada zumunta.
An dai zargi mutumin da fallasa hotunan ne bayan yunkurin neman kudi daga hannunta ya ci tura.
Ana zargin mutumin ya sayar da bidiyon tsiraicin budurwar ga mutanen da suka bukaci hakan akan Naira 3,000.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke wanda ake zargin bayan wacce abin ya faru da ita ta kai rahoto ofishin kwamishiniyar harkokin mata da walwalar yara Misis Ify Obinabo.