An kama sojan da harbe wani direban mota a jihar Borno

Aljazeera

Rundunar sojan Najeriya shiya ta 7 dake Maiduguri ta ce ta tsare wani soja da ake zargin yana da hannu kan kisan wani direban babbar mota akan hanyar Gamboru-Dikwa.

A wata sanarwa ranar Alhamis, A. Y Jingina mai magana da yawun rundunar ya ce lamarin ya faru a washegarin ranar Kirsimeti a wurin wani shingen binciken ababen hawa inda aka ajiye sojojin domin gudanar da aikinsu da suka saba.

Ya ce sojan da yake da hannu a faruwar lamarin an kama shi kuma tuni aka kaddamar da bincike.

Jingina ya ce bayan faruwar lamarin rundunar ta shiga tattaunawa kungiyar sufuri ta NURTW domin kare faruwar rikici.

Shima kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Usman Tar ya ce za ayi cikakke bincike kan faruwar lamarin tare da tabbatar da cewa an yi adalaci.

More from this stream

Recomended