An Kama Wani Shugaban Karamar Hukuma Da Ya Shirya Kashe Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Benue

Rundunar yan sandan Najeriya ta sanar da kama wani shugaban karamar hukuma a jihar Benue da kuma wani mutum guda inda ake zarginsu da kitsa kisan kai.

Rundunar ta ce ta samu nasarar kama mutanen biyu ne saboda ƙoƙarin jami’anta.

A wata sanarwa mai magana da yawun rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa shugaban karamar hukumar ya yi hayar wasu yan bindiga da niyar su hallaka shugaban majalisar dokokin jihar Benue, Hon. Aondona Hycenth Dajoh.

Adejobi ya ce biyo bayan samun kwararan bayanan sirri sashen tattara bayanan sirri da kuma rundunar kar ta kwana sun kama aiki gadan-gadan har ta kai ga kama mutanen biyu.

Kawo yanzu mutanen biyu na tsare a hedkwatar rundunar yan sandan inda suke cigaba da amsa tambayoyi.

More from this stream

Recomended