An kama mutane biyu da laifin karkatar da buhunan kayan tallafin abinci na gwamnatin Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da karkatar da kayan tallafin abinci da gwamnatin ta samar.

Mutanen da aka kama sun haɗa da mataimaki na musamman ga gwammnan Kano, Tasi’u Al’amin Roba da kuma Abdulƙadir Muhammad an kama su ne a wani ɗakin ajiye kayayyaki dake unguwar Sharaɗa a birnin Kano.

A cewar kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel an kama mutanen ne lokacin da suke sauya buhunan shinkafa da na Masara mai ɗauke da hoton gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya zuwa wasu buhunan na daban da babu hoto ko suna a jiki.

Kwamishinan ya ce rundunar ta kaddamar da bincike domin gano buhunan masara da na shinkafa nawa aka sauya buhu aka kuma sayar.

More from this stream

Recomended