An kama mutane biyu da laifin karkatar da buhunan kayan tallafin abinci na gwamnatin Kano

Rundunar Æ´an sandan jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da karkatar da kayan tallafin abinci da gwamnatin ta samar.

Mutanen da aka kama sun haÉ—a da mataimaki na musamman ga gwammnan Kano, Tasi’u Al’amin Roba da kuma AbdulÆ™adir Muhammad an kama su ne a wani É—akin ajiye kayayyaki dake unguwar SharaÉ—a a birnin Kano.

A cewar kwamishinan Æ´an sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel an kama mutanen ne lokacin da suke sauya buhunan shinkafa da na Masara mai É—auke da hoton gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya zuwa wasu buhunan na daban da babu hoto ko suna a jiki.

Kwamishinan ya ce rundunar ta kaddamar da bincike domin gano buhunan masara da na shinkafa nawa aka sauya buhu aka kuma sayar.

More News

Tinibu ya aikawa da majalisar dattawa sunaye 7 na  ministocin da zai naÉ—a

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta tabbatar da sunayen mutane 7 da ya tura majalisar da zai...

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...