An kama mai jagorantar sulhun sakin fasinjojin jirgin kasa na Abuja-Kaduna a kasar Masar

Rundunar yan sandan kasa da kasa ta kama, Mallam Tukur Mamu mamallakin jarida Desert Herald dake Kaduna.

Mamu shi ne mutumin da ya jagoranci tattaunawa tsakanin gwamnati da kuma yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasar da ya ta shi daga Abuja zuwa Kaduna.

An kama Mamu ne a filin jirgin saman birnin Alƙahira lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa kasar Saudiya.

Mamu ya fadawa jaridar Premium Times cewa ba a same shi da wani kayan laifi ba kuma tuni aka taso keyarsa zuwa Najeriya.

Ana sa ran zai iso filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ranar yau kuma zai ansa wasu tambayoyi daga jami’an hukumar DSS.

More from this stream

Recomended