An kama mai cin sassan jikin mutum a Gusau

Aminu Baba wani fitaccen mai sayar da motoci a Aminchi Motors dake Gusau ya fada hannun jami’an yan sanda inda ya bayyana musu irin munanan ayyukan da ya ke yi.


Baba ya fadawa yan sanda cewa yana ci tare da sayar da sassan jikin bil-adama ga wasu mutane da yaki fadin sunansu.
A makon da ya wuce ne ya fada hannun jami’an yan sanda kan laifin kisa da kuma gididdiba wani karamin yaro.


Ya bayyana cewa ya dauki wasu matasa biyu aiki domin nemowa tare da kashe masa kananan yara kuma sun yi masa haka har sau biyu inda ya basu kudi Naira miliyan daya.


“Na biya su 500,000 kan kisan kowane mutum daya cikin kananan yaran biyu. Muna cire azzakari,ido,hanji da makogwaro ina cin wadanannan sassan kana na sayar da ragowar ga masu bukatarsu.”


Abdulshakur Muhammad shi ne daya mutumin da ake zargi ya bayyana cewa wannan ne Karo na uku da Baba yake bashi kwangilar samo masa sassan jikin bil’adama.

More from this stream

Recomended